2 Ku kasa kunne ga tsawar muryarsa,Ku saurara ga maganarsa mai ƙarfi.
3 Yakan sako ta a ƙarƙashin samaniya duka,Walƙiyarsa takan zagaya dukan kusurwoyin duniya.
4 Bayan walƙiyar akan ji rugugin muryarsa,Ya yi tsawa da muryarsa ta ɗaukaka,Ko da yake an ji muryarsa bai dakatar da tsawar ba.
5 Muryar tsawar Allah mai banmamaki ce,Yana aikata manyan abubuwa da suka fi ƙarfin ganewarmu.
6 Yakan umarci dusar ƙanƙara ta fāɗo bisa duniya,Yayyafi da ruwan sama kuwa su yi ƙarfi.
7 Yakan tsai da kowane mutum daga aikinsa,Domin dukan mutane su san aikinsa.
8 Namomin jeji sukan shiga wurin kwanciyarsu,Su yi zamansu a ciki.