4 Bayan walƙiyar akan ji rugugin muryarsa,Ya yi tsawa da muryarsa ta ɗaukaka,Ko da yake an ji muryarsa bai dakatar da tsawar ba.
5 Muryar tsawar Allah mai banmamaki ce,Yana aikata manyan abubuwa da suka fi ƙarfin ganewarmu.
6 Yakan umarci dusar ƙanƙara ta fāɗo bisa duniya,Yayyafi da ruwan sama kuwa su yi ƙarfi.
7 Yakan tsai da kowane mutum daga aikinsa,Domin dukan mutane su san aikinsa.
8 Namomin jeji sukan shiga wurin kwanciyarsu,Su yi zamansu a ciki.
9 Guguwa takan taso daga inda take,Sanyi kuma daga cikin iska mai hurawa.
10 Numfashin Allah yakan sa ƙanƙara,Yakan sa manyan ruwaye su daskare farat ɗaya.