1 Ubangiji ya yi magana da Ayuba ta cikin guguwa.
2 “Wane ne wannan da yake ɓāta shawaraDa maganganu marasa ma'ana?
3 Ka tashi tsaye ka sha ɗamara kamar namiji,Zan yi maka tambaya, kai kuwa ka ba ni amsa.
4 A ina kake sa'ad da na aza harsashin gina duniya?Faɗa mini idan ka sani.