14 Yakan sāke kamar lakar da take ƙarƙashin hatimi,Yakan rine kamar riga.
15 Akan hana wa mugaye haske,Sa'ad da sukan ɗaga hannuwansu sama akan kakkarya su.
16 “Ko ka taɓa shiga cikin maɓuɓɓugan teku?Ka taɓa yin tafiya a cikin zurfin lallokin teku?
17 An taɓa nuna maka ƙofofin mutuwa?Ko kuwa ka taɓa ganin ƙofofin duhu ƙirin?
18 Ko ka san iyakar fāɗin duniya?Ka amsa mini in ka san dukan waɗannan.
19 “Ina hanya zuwa wurin da haske yake?A ina kuma duhu yake?
20 Ka san iyakarsa ko mafarinsa?