18 Ko ka san iyakar fāɗin duniya?Ka amsa mini in ka san dukan waɗannan.
19 “Ina hanya zuwa wurin da haske yake?A ina kuma duhu yake?
20 Ka san iyakarsa ko mafarinsa?
21 Ka sani, gama a lokacin nan an haife ka,Shekarunka kuwa suna da yawa.
22 “Ka taɓa shiga rumbunan dusar ƙanƙara?Ko kuwa ka taɓa shiga rumbunan ajiyar ƙanƙara?
23 Na adana su ne don lokacin wahala,Domin ranar faɗa da ta yaƙi.
24 Ina hanya zuwa inda rana take fitowa,Ko kuma ta inda iskar gabas take hurowa ta māmaye ko'ina?