2 “Wane ne wannan da yake ɓāta shawaraDa maganganu marasa ma'ana?
3 Ka tashi tsaye ka sha ɗamara kamar namiji,Zan yi maka tambaya, kai kuwa ka ba ni amsa.
4 A ina kake sa'ad da na aza harsashin gina duniya?Faɗa mini idan ka sani.
5 Wane ne ya zayyana kusurwoyinta?Hakika ka sani.Wane ne kuma ya auna ta?
6 A kan me aka kafa tushenta?Wa ya aza dutsen kan kusurwarta?
7 Sa'ad da taurarin asuba suka raira waƙa tare,Sai mala'iku duka suka yi sowa saboda murna.
8 “Wa ya yi wa teku iyakaSa'ad da ta tumbatso daga zurfafa?