25 “Wa ya haƙa hanyar da ruwan sama mai kwararowa zai bi?Da kuma hanyar da gatarin aradu zai bi?
26 Wa ya kuma kawo ruwan sama a ƙasar da ba mutane,Da a cikin hamada inda ba kowa,
27 Don a shayar da zozayar ƙasa inda ba kowa,Har ta tsiro da ciyayi?
28 “Ruwan sama yana da mahaifi?Wa ya haifi ɗiɗɗigar raɓa?
29 Wace ce mahaifiyar ƙanƙara?Wace ce kuma ta haifi jaura?
30 Ruwa ya daskare ya yi ƙarfi kamar dutse,Teku ta daskare.
31 “Za ka iya ɗaure sarƙoƙin kaza-da-'ya'yanta?Ko ka iya kwance igiyoyin mafarauci-da-kare-da-zomo?