26 Wa ya kuma kawo ruwan sama a ƙasar da ba mutane,Da a cikin hamada inda ba kowa,
27 Don a shayar da zozayar ƙasa inda ba kowa,Har ta tsiro da ciyayi?
28 “Ruwan sama yana da mahaifi?Wa ya haifi ɗiɗɗigar raɓa?
29 Wace ce mahaifiyar ƙanƙara?Wace ce kuma ta haifi jaura?
30 Ruwa ya daskare ya yi ƙarfi kamar dutse,Teku ta daskare.
31 “Za ka iya ɗaure sarƙoƙin kaza-da-'ya'yanta?Ko ka iya kwance igiyoyin mafarauci-da-kare-da-zomo?
32 Za ka iya bi da yaneyanen sararin sama bisa ga fasalinsu?