38 Sa'ad da ƙura ta murtuke ta taru jingim, ta game kam?
39 “Ka iya farauto wa zakoki abinci?Ko ka ƙosar da yunwar sagarun zakoki,
40 Sa'ad da suke fako a kogwanninsu,Ko suna kwance suna jira a maɓoyarsu?
41 Wa yake tanada wa hankaka abincinsa,Sa'ad da 'ya'yansa suke kuka ga Allah,Suna kai da kawowa saboda rashin abinci?”