6 A kan me aka kafa tushenta?Wa ya aza dutsen kan kusurwarta?
7 Sa'ad da taurarin asuba suka raira waƙa tare,Sai mala'iku duka suka yi sowa saboda murna.
8 “Wa ya yi wa teku iyakaSa'ad da ta tumbatso daga zurfafa?
9 Sa'ad da na suturta ta da gizagizai,Na yi mata maɗauri da duhu ƙirin.
10 Na sa mata iyakoki,Na sa mata ƙyamare da ƙofofi,
11 Na ce mata, ‘Iyakar inda za ki tsaya ke nan,Ba za ki wuce ba.Nan raƙuman ruwanki masu tumbatsa za su tsaya.’
12 “Ayuba, a dukan kwanakinkaKa taɓa umartar wayewar gari,Ko ka sa alfijir ya keto?