1 “Ka san lokacin da awakan dutse suke haihuwa?Ka taɓa lura da yadda batsiya take haihuwa?
2 Ka san ko watanni nawa suke yi kafin su haihu?Ka san lokacin haihuwarsu?
3 Ka san lokacin naƙudarsu, sa'ad da suke haihuwar 'ya'yansu,Lokacin da 'ya'yansu suke fita cikinsu?
4 'Ya'yansu sukan yi ƙarfi su girma a fili cikin saura,Sukan yi tafiyarsu ba su komawa wurin iyayensu.