11 Za ka dogara gare shi saboda tsananin ƙarfinsa?Za ka kuma bar masa aikinka?
12 Ka gaskata zai komo,Ya kawo maka hatsi a masussukarka?
13 “Jimina takan karkaɗa fikafikanta da alfarma!Amma ba su ne gashin fikafikan ƙauna ba.
14 Jimina takan bar wa ƙasa ƙwayayenta,Ta bar ƙasa ta ɗumama su.
15 Takan manta wani ya iya taka su su fashe,Ya yiwu kuma wani naman jeji ya tattake su.
16 Takan yi wa 'ya'yanta mugunta,Sai ka ce ba nata ba ne,Ko da yake ta sha wahala a banza,Duk da haka ba ta damu ba.
17 Gama Allah bai ba ta hikima ba,Bai kuwa ba ta fahimi ba.