2 Ka san ko watanni nawa suke yi kafin su haihu?Ka san lokacin haihuwarsu?
3 Ka san lokacin naƙudarsu, sa'ad da suke haihuwar 'ya'yansu,Lokacin da 'ya'yansu suke fita cikinsu?
4 'Ya'yansu sukan yi ƙarfi su girma a fili cikin saura,Sukan yi tafiyarsu ba su komawa wurin iyayensu.
5 “Wa ya bar jakin jeji ya yi yadda yake so?Wa ya ɓalle dabaibayin jaki mai sauri,
6 Wanda na ba fili fetal ya zama gidansa,Da ƙasa mai gishiri a wurin zamansa?
7 Yakan yi wa hayaniyar birane ba'a,Ba ruwansa da tsawar masu kora.
8 Tsaunukan duwatsu ne wurin kiwonsa,A can yake neman kowane ɗanyen abu.