6 Wanda na ba fili fetal ya zama gidansa,Da ƙasa mai gishiri a wurin zamansa?
7 Yakan yi wa hayaniyar birane ba'a,Ba ruwansa da tsawar masu kora.
8 Tsaunukan duwatsu ne wurin kiwonsa,A can yake neman kowane ɗanyen abu.
9 “Kutunkun ɓauna zai yarda ya yi maka aiki?Zai yarda ya kwana ɗaya a dangwalinka?
10 Ka iya ɗaure shi da igiya a kwarin kunya?Ko kuwa zai yi maka kaftu a fadamarka?
11 Za ka dogara gare shi saboda tsananin ƙarfinsa?Za ka kuma bar masa aikinka?
12 Ka gaskata zai komo,Ya kawo maka hatsi a masussukarka?