3 Ka koya wa mutane da yawa,Ka kuma ƙarfafa hannuwan marasa ƙarfi.
4 Idan wani ya yi tuntuɓe,Ya gaji, ya rasa ƙarfi,Kalmominka suka ƙarfafa zuciyarsa,Har ya iya tsayawa kyam.
5 Yanzu naka lokacin wahala ya zo,Kai kuwa ka rikice, ka kasa ɗaurewa,
6 Kana yi wa Allah sujada,Ba wani laifi a zamanka,Ya kamata ka amince ka sa zuciya.
7 “Yanzu fa sai ka yi tunani.Ka faɗi bala'i ɗaya wanda ya taɓa fāɗa wa adalin mutum.
8 Na taɓa ganin mutane suna huɗe gonar mugunta,Suna shuka mugunta,Suka kuwa girbe mugunta.
9 A cikin fushinsa Allah yakan hallaka su kamar hadiri.