13 Dukansu ka binne su a ƙasa,Ka ɗaure fuskokinsu, ka jefa su a lahira.
14 Sa'an nan ni kaina kuma zan sanar da kai,Cewa da hannun damanka za ka yi nasara.
15 “Ga dorina wanda ni na halicce ta,Kamar yadda na halicce ka,Tana cin ciyawa kamar sa.
16 Ga shi, ƙarfinta yana cikin ƙugunta,Ikonta yana cikin tsakar cikinta.
17 Na yi mata wutsiya miƙaƙƙiya, mai ƙarfi kamar itacen al'ul,Jijiyoyin cinyoyinta suna haɗe wuri ɗaya
18 Ƙasusuwanta bututun tagulla ne,Gaɓoɓinta kamar sandunan ƙarfe ne.
19 “Ita ce ta farko cikin ayyukan Allah,Sai Mahaliccinta kaɗai yake iya tunkararta da takobi!