1 “Ka iya kama dodon ruwa da ƙugiyar kama kifi?Ko kuma ka iya zarge harshensa da igiya?
2 Ka iya sa wa hancinsa asirka?Ko ka iya huda muƙamuƙinsa da ƙugiya?
3 Zai ta yi maka godo?Zai yi maka magana da tattausar murya?
4 Zai ƙulla alkawari da kai,Cewa zai zama baranka har abada?
5 Za ka yi wasa da shi kamar yadda za ka yi da tsuntsu?Ko za ka ɗaure shi da tsarkiya domin barorinka mata?
6 'Yan kasuwa za su saye shi?Za su karkasa shi ga fatake?