16 Suna haɗe da juna gam,Ko iska ba ta iya ratsa tsakaninsu.
17 Sun manne da juna har ba su rabuwa.
18 Atishawarsa takan walƙata walƙiya,Idanunsa kuma kamar ketowar alfijir.
19 Harsunan wuta kamar jiniya suna fitowa daga bakinsa,Tartsatsin wuta suna ta fitowa.
20 Hayaƙi na fita daga hancinsaKamar tururi daga tukunya mai tafasa,Ko bāgar da ta kama wuta.
21 Numfashinsa yakan kunna gawayi,Harshen wuta yana fita daga bakinsa.
22 A wuyansa ƙarfi yake zaune,Razana tana rausaya a gabansa.