18 Atishawarsa takan walƙata walƙiya,Idanunsa kuma kamar ketowar alfijir.
19 Harsunan wuta kamar jiniya suna fitowa daga bakinsa,Tartsatsin wuta suna ta fitowa.
20 Hayaƙi na fita daga hancinsaKamar tururi daga tukunya mai tafasa,Ko bāgar da ta kama wuta.
21 Numfashinsa yakan kunna gawayi,Harshen wuta yana fita daga bakinsa.
22 A wuyansa ƙarfi yake zaune,Razana tana rausaya a gabansa.
23 Namansa yana ninke, manne da juna,Gama ba ya motsi.
24 Zuciyarsa tana da ƙarfi kamar dutse,Ƙaƙƙarfa kamar dutsen niƙa.