5 Za ka yi wasa da shi kamar yadda za ka yi da tsuntsu?Ko za ka ɗaure shi da tsarkiya domin barorinka mata?
6 'Yan kasuwa za su saye shi?Za su karkasa shi ga fatake?
7 Za ka iya huhhuda fatarsa da zaguna?Ko kuwa kansa da māsu?
8 In ka kama shi, ka daɗe kana tunawa da yaƙin da ba za ka ƙara marmarin yi ba!
9 Ba ma amfani a yi ƙoƙarin kama shi,Tunanin yin haka ma abin tsoro ne.
10 Ba wani mai zafin hali da zai kuskura ya tsokane shi.Wane ne wannan da zai iya tsayawa a gabana?
11 Wa ya ba ni har da zan biya shi?Dukan abin da yake cikin duniyan nan nawa ne.