1 Ayuba ya amsa wa Ubangiji.
2 “Na sani kai kake da ikon yin dukan abu,Ba wanda ya isa ya hana ka yin abin da ka nufa.
3 Wane ne wannan marar ilimi da zai ɓoye shawara?Saboda haka na hurta abin da ban gane ba,Abubuwa waɗanda ban gane ba suna banmamaki ƙwarai.
4 Ka ce, ‘Kasa kunne, zan yi magana da kai,Zan yi maka tambaya, ka ba ni amsa.’
5 Dā jin labarinka nake,Amma yanzu na gan ka ido da ido.
6 Saboda haka na ga ni ba kome ba ne,Na tuba, ina hurwa da ƙura da toka.”