1 “Ka yi kira, ya Ayuba, ka gani, ko wani zai amsa!Akwai wani mala'ika da za ka juya zuwa gare shi?
2 Ba shi da amfani ka dami kankaHar ka mutu, saboda tsarguwa, gama wannan wawanci ne,Da aikin rashin hankali.
3 Na ga waɗansu wawaye waɗanda ake gani kamar suna zaune lafiya,Amma nan da nan sai na la'anci gidajensu.
4 Ko kaɗan, 'ya'yansu maza ba za su taɓa zama lafiya ba.Ba wanda zai tsaya musu a ɗakin shari'a.
5 Mayunwata za su ci amfanin gonar wawa,Har da hatsin da yake girma cikin ƙayayuwa,Waɗanda suke jin ƙishirwa za su ji ƙyashin dukiyarsa.