15 Amma Allah yakan ceci matalauta daga mutuwa,Yakan kuma ceci masu bukata daga zalunci.
16 Yakan sa matalauta su sa zuciya,Ya sa mugaye su yi shiru.
17 “Mai farin ciki ne mutumin da Allah ya hora,Kada ka tsargu sa'ad da ya tsauta maka.
18 Allah yakan yi maganin raunin da ya yi maka,Ciwon da ya ji maka da hannunsa,Da hannunsa yakan warkar.
19 Yakan tsare ka daga cuta sau shida har sau bakwai,Ba muguntar da za ta taɓa ka.
20 Yakan kiyaye ka da rai a lokacin yunwa,A yaƙi kuma yakan tsare ka daga mutuwa.
21 Allah yakan kuɓutar da kai daga ƙarairayi da ɓata suna,Yakan cece ka daga hallaka.