22 Aikin kama-karya da yunwa za su zama abin dariya a gare ka,Ba kuwa za ka ji tsoron namomin jeji ba.
23 Ba za a sami duwatsu a gonakin da kake nomawa ba,Mugayen namomin jeji ba za su far maka ba.
24 Sa'an nan za ka zauna lafiya a alfarwanka,A sa'ad da ka dubi tumakinka, za ka tarar suna nan lafiya.
25 'Ya'yanka za su yi yawa kamar ciyawa,Kamar yadda alkama take a lokacin kakarta.
26 Haka kai ma za ka rayu, har ka tsufa da kyakkyawan tsufa.