1 Ayuba ya amsa.
2 “In da za a auna wahalata da ɓacin raina da ma'auni,
3 Da sun fi yashin teku nauyi.Kada ka yi mamaki da maganganun da nake yi.
4 Allah Maɗaukaki ya harbe ni da kibau,Dafinsu kuwa ya ratsa jikina.Allah ya jera mini abubuwa masu banrazana.
5 “Idan jaki ya sami ciyawar ci, muradinsa ya biya,In ka ji saniya ta yi shiru, tana cin ingirici ne.