16-17 Rafin yana cike da iska mai laima da ƙanƙara,Amma lokacin zafi sai su ɓace,Kwacciyar rafin, sai ta bushe ba kome.
18 Ayari sukan ɓata garin neman ruwa,Su yi ta gilo, har su marmace a hamada.
19 Ayari daga Sheba da Tema suka yi ta nema,
20 Amma sa zuciyarsu ta ƙare a gefen busassun rafuffuka,
21 Kamar rafuffukan nan kuke a gare ni,Kun ga abin da ya same ni, kun gigita.
22 Na roƙe ku ku ba ni kyauta ne?Ko kuwa na roƙe ku ku ba wani rashawa domina?
23 Ko kuma na roƙe ku ku cece ni daga maƙiyi ko azzalumi ne?