4 Allah Maɗaukaki ya harbe ni da kibau,Dafinsu kuwa ya ratsa jikina.Allah ya jera mini abubuwa masu banrazana.
5 “Idan jaki ya sami ciyawar ci, muradinsa ya biya,In ka ji saniya ta yi shiru, tana cin ingirici ne.
6 Amma wane ne zai iya cin abinci ba gishiri?Akwai daɗin ɗanɗano ga farin ruwan ƙwai?
7 Ba na jin marmarin cin abinci irin haka,Kowane irin abu da na ci yakan sa mini cuta.
8 “Me ya sa Allah ya ƙi ba ni abin da nake roƙo?Me ya sa ya ƙi yin abin da nake so?
9 Da ma ya ci gaba kawai ya kashe ni,Ko ya sake ikonsa ya datse ni!
10 Da na san zai yi haka, da sai in yi tsalle don murna,Da ba zan kula da tsananin azabar da nake ciki ba.Ban taɓa yin gāba da umarnan Allah ba.