1 “Kamar kamen soja na tilas,Haka zaman 'yan adam take,Kamar zaman mai aikin bauta.
2 Kamar bawa ne wanda yake sa zuciya ga inuwa mai sanyi,Kamar ma'aikaci wanda yake sa zuciya ga lokacin biya.
3 Wata da watanni ina ta aikin banza,Kowane dare ɓacin rai yake kawo mini.
4 Sa'ad da na kwanta barci, sai daren ya daɗa tsawoIn yi ta jujjuyawa duk dare, in ƙosa gari ya waye.