3 Wata da watanni ina ta aikin banza,Kowane dare ɓacin rai yake kawo mini.
4 Sa'ad da na kwanta barci, sai daren ya daɗa tsawoIn yi ta jujjuyawa duk dare, in ƙosa gari ya waye.
5 Jikina cike yake da tsutsotsi,Ƙuraje duka sun rufe shi,Daga miyakuna mugunya tana ta zuba.
6 Kwanakina sun wuce ba sa zuciya,Sun wuce da sauri kamar ƙoshiyar saƙa.
7 “Ka tuna, ya Ubangiji, raina iska ne kawai,Farin cikina ya riga ya ƙare.
8 Kuna ganina yanzu, amma ba za ku sāke ganina ba.Idan kuka neme ni, za ku tarar ba na nan.
9 Kamar girgijen da yake bajewa ya tafi,Haka nan mutum yake mutuwa.