10 Amma ka yarda masu hikima na zamanin dā su koya maka,Ka kasa kunne ga abin da za su faɗa.
11 “Iwa ba ta tsirowa inda ba ruwa,Ba a taɓa samunta a ko'ina ba sai a fadama.
12 In ruwan ta ƙafe, ita ce za ta fara bushewa,Tun tana ƙanƙana ba ta isa a yanke a yi amfani da ita ba.
13 Marasa tsoron Allah kamar iwan nan suke,Ba su da sa zuciya muddin sun rabu da Allah.
14 Suna dogara ga silin zare, murjin gizo-gizo.
15 Idan suka jingina ga saƙar gizo-gizo, za ta iya tokare su?Idan sun kama ta, za ta taimake su tsayawa?
16 “Mugaye sukan tsiro kamar ciyayi a hasken rana,Ciyayin da sukan yaɗu su cinye gona duka.