3 Allah bai taɓa yin danniya ba,Bai kuma taɓa fāsa aikata abin da yake daidai ba.
4 Lalle 'ya'yanka sun yi wa Allah zunubi,Don haka ya hukunta su yadda ya cancanta.
5 Amma sai ka juyo ka yi roƙo ga Allah Maɗaukaki.
6 Idan kana da tsarki da aminci, Allah zai taimake ka,Ya maido da iyalin gidanka, ya yi maka sakayya.
7 Duk hasarar dukiyan nan da ka yi, ba kome ba neIn aka gwada da abin da Allah zai ba ka nan gaba.
8 “Ka tsai da zuciyarka a kan hikima irin ta zamanin dā.Ka kuma yi ta yin tunani a kan gaskiyar da kakanninmu suka koya.
9 Kwanakinmu 'yan kaɗan ne kawai,Ba mu san kome ba,Mu inuwa ne kawai a fuskar duniya.