1 Ayuba ya amsa.
2 “Ai, na taɓa jin waɗannan duka,Amma ta ƙaƙa mutum zai yi jayayya da Allah har ya yi nasara?
3 Ta ƙaƙa za ka iya jayayya da shi?Yana yiwuwa ya yi maka tambayoyi guda dubuWaɗanda ba wanda zai iya ba da amsarsu.
4 Allah mai hikima ne, mai iko,Ba wanda zai iya ja in ja da shi.
5 Yakan kawar da manyan duwatsu farat ɗaya,Ya hallaka su da fushinsa,
6 Allah yakan aiko da girgizar ƙasa, ya girgiza duniya,Yakan jijjiga ginshiƙan da duniya take zaune a kansu.