4 Allah mai hikima ne, mai iko,Ba wanda zai iya ja in ja da shi.
5 Yakan kawar da manyan duwatsu farat ɗaya,Ya hallaka su da fushinsa,
6 Allah yakan aiko da girgizar ƙasa, ya girgiza duniya,Yakan jijjiga ginshiƙan da duniya take zaune a kansu.
7 Allah yana da iko ya hana rana fitowa,Ko kuma ya hana taurari haskakawa da dare.
8 Ba wanda ya taimaki Allah shimfiɗa sammai,Wanda yake taka raƙuman ruwan teku, ya kuma kwantar da su.
9 Allah ya rataye taurari a sararin sama,Wato su mafarauci da kare da zomo,Da kaza da 'ya'yanta da taurarin kudu.
10 Ba shi yiwuwa mu gane manyan abubuwa da yake yi.Ayyukan al'ajabansa ba su da iyaka.