8 Na ji, amma ban gane ba. Sai na ce, “Ya shugabana, mene ne ƙarshen waɗannan abubuwa?”
9 Sai ya ce, “Yi tafiyarka, Daniyel, gama an rufe wannan magana, an kuma kulle ta har ƙarshen lokaci.
10 Mutane da yawa za su tsarkake kansu, su zama masu tsabta tsab tsab, amma mugaye ba za su gane ba, za su yi ta muguntarsu, amma masu hikima za su gane.
11 “Tun daga lokacin da za a hana miƙa hadayar ƙonawa ta yau da kullum, a kafa abin banƙyama, wanda yake lalatarwa, za a yi kwana dubu da ɗari biyu da tasa'in.
12 Masu farin ciki ne waɗanda suka daure, har suka kai ƙarshen kwana dubu da ɗari uku da talatin da biyar.
13 “Ka yi tafiyarka ka huta, a ƙarshen kwanaki za ka tashi ka karɓi naka rabo.”