29 “Ya maigirma, sa'ad da kake kwance a gadonka sai tunanin abin da zai faru nan gaba ya zo maka. Shi kuma wanda yake bayyana asirai ya sanar da kai abin da zai faru nan gaba.
30 Amma ba a bayyana mini wannan asiri saboda ina da wata hikima fiye da sauran mutane ba, sai dai domin a sanar wa sarki da fassarar, ka kuma san tunanin da ya shiga zuciyarka.
31 “Ya sarki, ka ga wani babban mutum-mutum mai walƙiya, mai bantsoro, yana tsaye a gabanka.
32 An yi kan mutum-mutumin da zinariya tsantsa. Ƙirji da damutsa, an yi su da azurfa, cikinsa da cinyoyinsa, an yi su da tagulla.
33 Da baƙin ƙarfe aka yi sharaɓansa, an yi ƙafafunsa da baƙin ƙarfe gauraye da yumɓu.
34 Sa'ad da kake cikin dubawa, sai aka gutsuro wani dutse ba da hannun mutum ba, aka bugi ƙafafunsa na baƙin ƙarfe gauraye da yumɓu, aka ragargaza shi.
35 Sa'an nan baƙin ƙarfen, da yumɓun, da tagullar, da azurfar, da zinariyar suka ragargaje gaba ɗaya, duka suka zama kamar ƙaiƙayi na masussuka da kaka. Iska kuwa ta kwashe su ta tafi da su, har ba a iya ganin ko alamarsu. Amma wannan dutse da ya buge mutum-mutumin ya girke, ya zama babban dutse ya cika duniya duka.