3 Sarki kuwa ya ce musu, “Na yi mafarki, na kuwa matsu ƙwarai in san mafarkin.”
4 Sai Kaldiyawa suka yi magana da sarki da Aramiyanci, suka ce, “Ran sarki ya daɗe! Ka faɗa wa barorinka mafarkin, za mu kuwa yi maka fassararsa.”
5 Sai sarki ya amsa wa Kaldiyawa, ya ce, “Na mance da abin, idan ba ku tuno mini da mafarkin, duk da fassararsa ba, to, za a daddatse ku gunduwa gunduwa, a mai da gidajenku juji.
6 Amma idan kun tuna mini mafarkin, duk da fassararsa, to, zan ba ku lada, da kyautai, da girma mai yawa. Don haka sai ku faɗa mini mafarkin, duk da fassararsa.”
7 Suka amsa, suka ce, “Bari sarki ya faɗa wa barorinsa mafarkin, mu kuwa za mu yi maka fassararsa.”
8 Sarki kuwa ya amsa ya ce, “Na sani kuna ƙoƙari ku ɓata lokaci ne kawai domin kun ga na manta da abin.
9 Idan ba ku tuno mini da mafarkin ba, hukuncin kisa ne yake jiranku. Kun haɗa kai don ku yi mini maganganun ƙarya na wofi har lokaci ya wuce. Sai ku faɗa mini mafarkin, ta haka kuwa zan sani za ku iya yi mini fassararsa.”