2 Na ga ya yi kyau in sanar muku da alamu da abubuwan al'ajabi waɗanda Allah Maɗaukaki ya nuna mini.
3 “Alamunsa da girma suke!Al'ajabansa da bantsoro suke!Sarautarsa ta har abada ce,Mulkinsa kuma daga zamani zuwa zamani ne.
4 “Ni, Nebukadnezzar ina cikin gidana, ina nishaɗi a fādata.
5 Sa'ad da nake kwance a gādona, sai na yi mafarki wanda ya tsorata ni. Tunanina da wahayi suka firgitar da ni.
6 Don haka na umarta a kirawo mini dukan masu hikima na Babila don su yi mini fassarar mafarkin.
7 Sai masu sihiri, da masu dabo, da Kaldiyawa, da masu duba suka zo, na faɗa musu mafarkin, amma ba su iya yi mini fassararsa ba.
8 Daga baya sai Daniyel wanda aka laƙaba wa suna Belteshazzar, wato irin sunan allahna, yana kuwa da ruhun alloli tsarkaka, ya shigo wurina. Na kuwa faɗa masa mafarkin, na ce,