20 Amma sa'ad da ya kumbura, ya taurare ransa yana ta yin girmankai, sai aka kore shi daga gadon sarautarsa, aka raba shi kuma da darajarsa.
21 Aka kore shi daga cikin mutane, aka ba shi hankali irin na dabba. Ya tafi ya zauna tare da jakunan jeji, yana ta cin ciyawa kamar sa. Jikinsa ya jiƙe da raɓa, har zuwa lokacin da ya gane, ashe, Allah Maɗaukaki ne yake sarautar 'yan adam, yakan kuma ba da ita ga wanda ya ga dama.
22 “Kai kuma Belshazzar, da kake ɗansa, ka san wannan duka, amma ba ka ƙasƙantar da kanka ba.
23 Maimakon haka, sai ka nuna wa Ubangiji girmankai, har ka sa aka kawo maka, kai da fādawanka, da matanka, da ƙwaraƙwaranka, tasoshin Haikalin Ubangiji, kuka sha ruwan inabi a cikinsu. Kuka yabi gumakan zinariya da na azurfa, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na itace, da na dutse waɗanda ba su ji, ba su gani, ba su da ganewar kome. Amma ba ka girmama Allah ba, wanda ranka da dukan harkokinka suna a hannunsa.
24 “Domin haka Allah ya aiko da wannan hannu da ya yi rubutun nan.
25 Wannan shi ne rubutun da aka yi, MENE, MENE, TEKEL, da UPHARSIN.
26 Ma'anar wannan ita ce, MENE, wato Allah ya sa kwanakin mulkinka su ƙare, sun kuwa ƙare.