10 Esta ba ta riga ta bayyana asalin mutanenta, da danginta ba, gama Mordekai ya umarce ta kada ta yi.
11 Kowace rana Mordekai yakan zo shirayin gidan matan kulle don ya san yadda Esta take.
12 Sa'ad da lokacin kowace budurwa ya yi da za ta shiga wurin sarki Ahasurus, bayan da ta riga ta yi wata goma sha biyu na ka'idar yin kwalliyar mata, wato takan shafe jiki da man ƙanshi wata shida, ta kuma shafe jiki da turare da man shafawa wata shida,
13 sa'an nan budurwar za ta shiga wurin sarki, sai a ba ta dukan abin da take bukata ta ɗauko daga gidan matan kullen zuwa fādar sarki.
14 Takan tafi da yamma, ta koma gidan matan kulle na biyu da safe, a hannun Shawashgaz, bābā na sarki, wanda yake lura da ƙwaraƙwarai. Ba za ta ƙara zuwa wurin sarki ba, sai ko ta sami farin jini a wurin sarki sa'an nan a kirawo ta.
15 Sa'ad da lokacin Esta 'yar Abihail, kawun Mordekai, wadda Mordekai ya karɓe ta tankar 'yarsa, ya yi da za ta shiga wurin sarki, ba ta bukaci kome ba, sai dai abin da Hegai, bābā na sarki, wanda yake lura da mata, ya ce. Esta kuwa tana da farin jini a idon duk wanda ya gan ta.
16 Sa'ad da aka kai Esta wurin sarki Ahasurus a fādarsa a wata na goma, wato watan Tebet, a shekara ta bakwai ta sarautarsa,