1 A kan rana ta uku sai Esta ta sa rigunan sarautarta, ta tafi, ta tsaya a shirayi na ciki na fādar sarki, kusa da ɗakin sarki. Sarki kuwa yana zaune a gadon sarautarsa, a gidan sarautarsa, daura da ƙofar shiga fāda.
2 Sa'ad da ya ga Esta tana tsaye a shirayin, sai ya miƙa mata sandan zinariya na sarauta, gama ta sami kwarjini a wurinsa. Sai Esta ta matsa kusa ta taɓa kan sandan.
3 Sarki ya ce mata, “Mene ne, sarauniya Esta? Me kike so? Za a ba ki, ko rabin mulkina ma.”
4 Sai Esta ta ce, “Idan sarki ya yarda, bari sarki ya zo tare da Haman yau wurin liyafa da na shirya wa sarki.”