Esta 8:8-14 HAU

8 Sai ku rubuta doka yadda kuke so da sunan sarki zuwa ga Yahudawa. Ku hatimce ta da hatimin zoben sarki, gama dokar da aka rubuta da sunan sarki, aka kuma hatimce ta da hatimin zoben sarki, ba za a iya a soke ta ba.”

9 A wannan lokaci aka kirawo magatakardun sarki ran ashirin da uku ga watan uku, wato watan Siwan. Bisa ga umarnin Mordekai aka rubuta doka zuwa ga Yahudawa, da shugabannin mahukunta, da masu mulki, da shugabannin larduna, tun daga Hindu har zuwa Habasha, wato lardi ɗari da ashirin da bakwai. Aka rubuta wa kowane lardi da irin rubutunsa, kowaɗanne mutane kuma da irin harshensu, zuwa ga Yahudawa kuma da irin rubutunsu da harshensu.

10 An yi rubutu da sunan sarki Ahasurus, aka kuma hatimce shi da hatimin zoben sarki. Aka aika da wasiƙun ta hannun 'yan-kada-ta-kwana, waɗanda suka hau dawakai masu zafin gudu da akan mora a aikin sarki.

11 A wasiƙun, sarki ya yardar wa Yahudawan da suke a kowane birni su taru, su kāre rayukansu, su kuma hallaka kowace rundunar mutane da kowane lardi da zai tasar musu, da 'ya'yansu, da matansu, su karkashe su, su rurrushe su, su kuma washe dukiyarsu.

12 Za a yi wannan a dukan lardunan sarki Ahasurus ran goma sha uku ga watan goma sha biyu, wato watan Adar.

13 Sai a ba kowane lardi fassarar dokar, don a yi shelarta ga dukan mutane, Yahudawa kuwa su yi shiri saboda wannan rana, domin su ɗau fansa a kan maƙiyansu.

14 Sai 'yan-kada-ta-kwana suka hau dawakai masu zafin gudu waɗanda akan mora a aikin sarki, suka tafi da gaggawa don su iyar da dokar sarki. Aka yi shelar dokar a Shushan, masarauta.