18 Ma'aseya, da Eliyezer, da Yarib, da Gedaliya iyalin Yeshuwa ɗan Yehozadak, su ne firistocin da suka auri mata baƙi.
19 Sai suka yi alkawari, cewa za su saki matansu. Suka ba da rago don yin hadaya saboda laifinsu.
20-24 Na iyalin Immer, Hanani, da ZabadiyaNa iyalin Harim, Ma'aseya, da Iliya, da Shemaiya, da Yehiyel, da UzziyaNa iyalin Fashur, Eliyehoyenai, da Ma'aseya, da Isma'ilu, da Netanel, da Yozabad, da ElasaNa Lawiyawa, Yozabad, da Shimai, da Kelaya, wato Kelita, da Fetahiya, da Yahuza, da EliyezerNa mawaƙa, EliyashibNa masu tsaron ƙofa, Shallum, da Telem, da Uri
25-33 Akwai kuma waɗansu na Isra'ila.Na iyalin Farosh, Ramiya, da Izziya, da Malkiya, da Miyamin, da Ele'azara, da Malkiya, da BenaiyaNa iyalin Elam, Mattaniya, da Zakariya, da Yehiyel, da Abdi, da Yeremot, da IliyaNa iyalin Zattu, Eliyehoyenai, da Eliyashib, da Mattaniya, da Yeremot, da Zabad, da AzizaNa iyalin Bebai, Yehohanan,da Hananiya, da Zabbai, da AtlaiNa iyalin Bani, Meshullam, da Malluki, da Adaya, da Yashub, da Sheyal, da YeremotNa iyalin Fahat-mowab, Adana, da Kelal, da Benaiya, da Ma'aseya, da Mattaniya, da Bezalel, da Binnuyi, da ManassaNa iyalin Harim, Eliyezer, da Isshiya, da Malkiya, da Shemaiya, da Shimeyon, da Biliyaminu, da Malluki, da ShemariyaNa iyalin Hashum, Mattenai, da Mattatta, da Zabad, da Elifelet, da Yeremai, da Manassa, da Shimai
34-37 Na iyalin Bani, Mayadi, da Amram, da Yuwel, da Benaiya, da Bedeya, da Keluhi, da Waniya, da Meremot, da Eliyashib, da Mattaniya, da Mattenai, da Yawasu
38-42 Na iyalin Binnuyi, Shimai, da Shelemiya, da Natan, da Adaya, da Maknadebai, da Shashai, Sharai, da Azarel, da Shelemiya, da Shemariya, da Shallum, da Amariya, da Yusufu
43 Na iyalin Nebo, Yehiyel, da Mattitiya, da Zabad, da Zebina, da Yaddai, da Yowel, da Benaiya