Ezra 2:1-36-39 HAU

1 Waɗannan su ne mutanen da suka bar lardin Babila suka komo Urushalima da Yahuza daga bautar talala da Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya kai su Babila. Kowa ya koma garinsu.

2 Sun komo tare da Zarubabel, da Yeshuwa, da Nehemiya, da Seriya, da Re'elaya, da Mordekai, da Bilshan, Misfar, da Bigwai, da Rehun, da Ba'ana.Ga jerin iyalan Isra'ila, da yawan waɗanda suka komo na kowane iyali daga zaman talala.

3-20 Zuriyar Farosh, mutum dubu biyu da ɗari da saba'in da biyu (2,172)Zuriyar Shefatiya, mutum ɗari uku da saba'in da biyuZuriyar Ara,mutum ɗari bakwai da saba'in da biyarZuriyar Fahat-mowab na zuriyar Yeshuwa da Yowab, mutum dubu biyu da ɗari takwas da goma sha biyu (2,812)Zuriyar Elam, mutum dubu da ɗari biyu da hamsin da huɗu (1,254)Zuriyar Zattu, mutum ɗari tara da arba'in da biyarZuriyar Zakkai, mutum ɗari bakwai da sittinZuriyar Bani, mutum ɗari shida da arba'in da biyuZuriyar Bebai, mutum ɗari shida da ashirin da ukuZuriyar Azgad, mutum dubu da ɗari biyu da ashirin da biyu (1,222)Zuriyar Adonikam, mutum ɗari shida da sittin da shidaZuriyar Bigwai, mutum dubu biyu da hamsin da shida (2,056)Zuriyar Adin, mutum ɗari huɗu da hamsin da huɗuZuriyar Ater na Hezekiya, mutum tasa'in da takwasZuriyar Bezai, mutum ɗari uku da ashirin da ukuZuriyar Yora, mutum ɗari da goma sha biyuZuriyar Hashum, mutum ɗari biyu da ashirin da ukuZuriyar Gibeyon, mutum tasa'in da biyar

21-35 Mutanen da suke a garuruwan nan, su ma suka komo.Mutanen Baitalami, mutum ɗari da ashirin da ukuMutanen Netofa, mutum hamsin da shidaMutanen Anatot, mutum ɗari da ashirin da takwasZuriyar Azmawet, mutum arba'in da biyuZuriyar Kiriyat-yeyarim, da Kefira, da Biyerot, mutum ɗari bakwai da arba'in da ukuZuriyar Rama da Geba, mutum ɗari shida da ashirin da ɗayaMutanen Mikmash, mutum ɗari da ashirin da biyuMutanen Betel da Ai, mutum ɗari biyu da ashirin da ukuZuriyar Nebo, mutum hamsin da biyuZuriyar Magbish, mutum ɗari da hamsin da shidaZuriyar wancan Elam, mutum dubu da ɗari biyu da hamsin da huɗu (1,254)Zuriyar Harim, mutum ɗari uku da ashirinZuriyar Lod, da Hadid, da Ono, mutum ɗari bakwai da ashirin da biyarMutanen Yariko, mutum ɗari uku da arba'in da biyarZuriyar Senaya, mutum dubu uku da ɗari shida da talatin (3,630)

36-39 Ga kuma lissafin iyalan firistocin da suka komo,Zuriyar Yedaiya na gidan Yeshuwa, mutum ɗari da saba'in da ukuZuriyar Immer, mutum dubu da hamsin da biyu (1,052)Zuriyar Fashur,mutum dubu da ɗari biyu da arba'in da bakwai (1,247)Zuriyar Harim, mutum dubu da goma sha bakwai (1,017)