9 Suka taso daga Babila a rana ta fari ga watan fari, suka iso Urushalima a rana ta fari ga watan biyar, Allah kuwa yana tare da su.
10 Gama Ezra ya ba da kansa ga yin nazarin dokokin Allah, ya kiyaye su, ya kuma koyar wa Isra'ilawa dokoki da farillan Allah.
11 Wannan ita ce takardar doka da sarki Artashate ya ba Ezra, wanda yake firist da magatakarda, ƙwararre cikin sha'anin dokoki da umarnan Ubangiji a cikin Isra'ilawa.
12 Ta ce, “Daga Artashate, sarkin sarakuna, zuwa ga Ezra firist, masanin shari'ar Allah na Sama.
13 “Yanzu na yi doka, cewa kowane mutum daga cikin mutanen Isra'ila, da firistocinsu, da Lawiyawansu da suke cikin mulkina wanda yake so ya koma Urushalima, sai ya tafi tare da kai.
14 Gama sarki ne da 'yan majalisarsa guda bakwai suka aike ka don ka san irin zaman mutanen Yahuza da na Urushalima game da dokokin Allahnka, waɗanda suke a hannunka,
15 domin kuma ka ba da azurfa da zinariya waɗanda sarki da 'yan majalisarsa suka ba Allah na Isra'ila da yardar ransu, wato Allah wanda Haikalinsa yake a Urushalima,