7 Mabartanka za su tasar maka nan da nan,Waɗanda suke binka bashi za su farka.Za ka zama ganima a gare su.
8 Saboda ka washe al'umman duniya da yawa,Sauran mutanen duniya duka za su washe ka,Saboda jinin mutane, da wulakancin da ka yi wa duniya,Da birane, da mazauna a cikinsu.
9 “Tasa ta ƙare, shi wanda ya arzuta gidansa da ƙazamar riba,Ya kuma gina gidansa a bisa don ya tsere wa masifa!
10 Ka jawo wa gidanka kunya,Saboda ka karkashe mutane da yawa,Ka hallaka kanka da kanka.
11 Dutse zai yi kuka daga garu,Katako kuwa zai amsa masa daga aikin da aka yi da itace.
12 “Tasa ta ƙare, shi wanda ya gina gari da jini,Ya kuma kafa birni da mugunta!
13 Ba Ubangiji Mai Runduna ne ya sa mutanen duniya, su yi wahala, wuta ta cinye ba?Sun kuma gajiyar da kansu a banza?