5 da ƙasar Gebaliyawa, da dukan Lebanon wajen gabas daga Ba'al-gad a gindin Dutsen Harmon zuwa iyakar Hamat,
6 da dukan mazaunan ƙasar tuddai, tun daga Lebanon zuwa Misrefot-mayim har da dukan Sidoniyawa. Ni da kaina zan kore su a gaban jama'ar Isra'ila. Kai kuwa za ka raba wa Isra'ilawa ƙasar ta zama gādonsu kamar yadda na umarce ka.
7 Yanzu fa sai ka raba wa kabilai tara da rabi ɗin nan ƙasar ta zama gādonsu.”
8 Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin kabilar Manassa, sun karɓi nasu gādo wanda Musa ya ba su a hayin Urdun wajen gabas. Abin da Musa, bawan Ubangiji, ya ba su ke nan,
9 daga Arower wadda take a gefen kwarin Arnon da birnin da yake tsakiyar kwarin, da dukan ƙasar tudu ta Medeba zuwa Dibon,
10 da dukan biranen Sihon, Sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulki a Heshbon, har zuwa iyakar Amoriyawa,
11 da Gileyad, da yankin ƙasar Geshuriyawa, da Ma'akatiyawa, da dukan Dutsen Harmon, da dukan Bashan, zuwa Salka,