1 Rabon da aka ba jama'ar Yahuza bisa ga iyalansu ya yi kudu, a iyakar Edom zuwa jejin Zin, can kudu nesa.
2 Iyakarsu wajen kudu ta miƙa tun daga ƙarshen Tekun Gishiri, daga wajen gaɓar da ta fuskanci kudu.
3 Ta milla kudanci hawan Akrabbim, ta zarce zuwa Zin, ta haura kudu da Kadesh-barneya, ta wajen Hesruna har zuwa Addar. Sai ta karkata zuwa Karka.
4 Ta zarce zuwa Azemon, ta bi ta rafin Masar zuwa inda ya gangara a teku. Wannan ita ce iyakar mutanen Yahuza wajen kudu.