11 Iyakar kuma ta biya wajen kafaɗar tudun, arewa da Ekron, sa'an nan ta karkata zuwa Shikkeron, ta wuce zuwa Dutsen Ba'ala, ta tafi zuwa Yabneyel, sa'an nan ta gangara a teku.
12 Bakin Bahar Rum, ita ce iyaka a wajen yamma. Wannan ita ce iyakar da ta kewaye jama'ar Yahuza bisa ga iyalansu.
13 Kamar yadda Ubangiji ya umarci Joshuwa, ya ba Kalibu, ɗan Yefunne, rabonsa a tsakiyar jama'ar Yahuza. Rabon da aka ba shi, shi ne Kiriyat-arba, wato Hebron. Arba shi ne uban Anak.
14 Daga can sai Kalibu ya kori 'ya'yan Anak, maza, su uku, da Sheshai, da Ahiman, da Talmai, zuriyar Anak.
15 Daga can kuma ya tafi ya fāɗa wa mazaunan Debir, dā sunan Debir Kiriyat-sefer ne.
16 Kalibu ya ce, “Duk wanda ya bugi Kiriyat-sefer, har ya ci ta, zan ba shi 'yata Aksa aure.”
17 Otniyel kuwa, ɗan Kenaz, ɗan'uwan Kalibu, ya ci Kiriyat-sefer. Kalibu kuwa ya ba shi Aksa 'yarsa aure.