14 Daga wajen arewa iyakar ta juya zuwa Hannaton, sa'an nan ta faɗa a kwarin Iftahel.
15 Waɗannan garuruwa, da Kattat, da Nahalal, da Shimron, da Idala, da Baitalami, suna cikin garuruwa goma sha biyu da ƙauyukansu da suke cikin yankin ƙasar kabilar Zabaluna.
16 Waɗannan su ne garuruwa da ƙauyukansu da suke cikin gādon mutanen Zabaluna bisa ga iyalansu.
17 Kuri'a ta huɗu ta faɗo a kan kabilar Issaka bisa ga iyalanta.
18 Garuruwan da suke cikin yankin ƙasar su ne, Yezreyel, da Kesullot, da Shunem,
19 da Hafarayim, da Shiyon, da Anaharat,
20 da Rabbit, da Kishiyon, da Ebez,