42 da Shalim, da Ayalon, da Itla,
43 da Elon, da Timna, da Ekron,
44 da Elteki, da Gebbeton, da Ba'alat,
45 da Yahud, da Bene-berak, da Gat-rimmon,
46 da Meyarkon, da Rakkon, tare da karkarar da take gefen Yaffa.
47 Sa'ad da Danawa suka rasa karkararsu, suka tafi, suka yaƙi Leshem. Da suka ci ta, sai suka hallaka mutanenta da takobi, suka mallaki ƙasar, suka zauna a ciki. Suka kuma sa wa Leshem, sunan kakansu, wato Dan.
48 Waɗannan garuruwa da ƙauyukansu su ne gādon kabilar Dan bisa ga iyalanta.